Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, hoton wasu kananan yara guda biyu da suke haddar kur’ani mai tsarki da mahaifiyarsu, ya dauki hankulan jama’a sosai.
A cikin wannan bidiyo, yara biyu suna karatun ayoyi daga surorin Al-Baqarah, Kausar, Abs, Nas, Qalam da Takweer.