Wakilai 76 daga kasashe 52 ne suka fafata a bangarori biyu na karatun kur'ani da haddar. A cewar Bernama, maza 24 da mata 12 ne ke fafatawa a gasar karatun da ake yi da yamma, kuma maza 27 da mata 13 a bangaren haddar da ake shiryawa da safe.
Ana watsa dukkan abubuwan da suka faru kai tsaye daga shafukan sada zumunta na Sashen Cigaban Musulunci na Malaysia (JAKIM). Za a kammala gasar ne a ranar 24 ga watan Agusta.