IQNA

Jirgion Kasa na daukar masu ziyarar arbaeen na farko ya tashi daga Basra

15:30 - August 24, 2023
Lambar Labari: 3489699
Bagadaza (IQNA) Ma'aikatar Sufuri ta kasar Iraki ta sanar da tashin jirgin kasa na farko daga Basra zuwa Karbala domin jigilar masu ziyarar Arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-Furat ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar sufurin kasar Iraki ta sanar da tashin jirgin kasa na farko daga birnin Basra zuwa Karbala Mu'ala domin jigilar masu ziyara Arba'in na Imam Hussain.

A cikin sanarwar da ma'aikatar sufurin kasar Iraki ta fitar a jiya Laraba, an bayyana cewa, shirin na musamman na hidimar Arbaeen, wanda ke karkashin kulawar Razzak Mohibs Al-Saadawi, ministan harkokin sufuri na kasar Iraki, ya hada da samar da jiragen kasa sama da 16 da za a yi amfani da su a kasar a  jigilar masu ziyara daga sassa daban-daban zuwa birnin Karbala.

Wannan bayanin ya kara da cewa: Kamfanin sufuri na kasar Iraki ya yi jigila ta farko daga lardin Basra zuwa lardin Karbala domin jigilar masu ziyarai.

A cewar wannan sanarwa, ministan sufurin na Iraki ya jaddada wajabcin kasancewar jami'an da abin ya shafa domin kawar da duk wani cikas wajen aiwatar da wannan shiri.

 

 

4164569

 

 

captcha