IQNA

An raba kwafin Kur'ani ga masu ziyarar Arbaeen na kasashen waje

19:13 - September 08, 2023
Lambar Labari: 3489779
Karbala (IQNA) Dakarun rundunar sojin sa kai Iraki na Haydaryoun Brigade sun gabatar da kwafin kur'ani mai tsarki ga mazuyarta  'yan kasashen waje tare da nuna darajar littafin Allah.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sabrin News cewa, daya daga cikin kyawawan al’amuran ziyarar Arba’in na bana a Karbala shi ne bankwana da kur’ani da ‘yan Iraqi suka yi wa maziyarat na kasashen waje.

A daren jiya masu ziyara daga Iran da nahiyar Afirka da wasu sassa na duniya sun yi bankwana da tarurrukan masoya ahlul bait tare da karbar kyautar kwafin kur’ani da dakarun rundunar Heydar suka raba.

Al'ummar Iraki sun dauki daren Arba'in a matsayin sa'o'i na karshe na hidima ga masu ziyara, kuma a cikin daren jiya sun nuna daraja da daukakar musulmi da kuma abubuwansu masu tsarki musamman kur'ani mai tsarki ta hanyar ba da kyautar kwafin kur'ani ga masu ziyara.

Tattakin Al-Haidariun Brigade na daya daga cikin manyan jerin gwanon hidimar maziyarta a Karbala.

Al-Haidriun Brigade na daya daga cikin reshen kungiyar Al-Hashd al-Shaabi, da suka kawo karshen ta’addancin ‘yan ta’adda na kungiyar ISIS a kasar Iraki.

 

4167320

 

captcha