Zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinu da yin Allah wadai da gwamnatin Isra'ila ta bazu a yawancin kasashen musulmi bayan sallar Juma'a.
An bayar da rahoton gudanar da gangami a Iran, Turkiyya, Masar, Jordan, Lebanon, Syria, Qatar, Iraq, Yemen, Malaysia da sauran wurare, a fiye da birni daya a wasu kasashen.