IQNA

Hosseini dan kasar Iran yana karanta ayoyi daga surorin Insan, Zilzal

TEHRAN (IQNA) – Sayyid Mohammad Jawad Hosseini makarancin kur’ani ne na kasar Iran wanda kasashen duniya suka amince da shi.

Hosseini wanda ya fito daga lardin Khorasan Razavi da ke arewa maso gabashin kasar Iran, ya samu matsayi da dama a gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa, ciki har da lambar yabo mafi girma a gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa ta Iran.

A baya-bayan nan ya karanta ayoyi na 1-18 a cikin suratu Insan da kuma ayoyin Zilzal a cikin wani shiri na kur’ani da aka gudanar a hubbaren Imam Rida (AS) da ke birnin Mashhad.

A nan za a iya sauraren karatunsa a cikin shirin: