Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-Masrawi cewa, karatun dan kasar Masar mai kayatarwa daga aya ta 16 zuwa ta 19 a cikin suratul Qaf a cikin shirin “Duniya wadin” a gidan talabijin din ya dauki hankulan mutane sosai. Wannan yaro dan kasar Masar da ke zaune a lardin Manoufiyah ya karanta wadannan ayoyi na suratul Mubarakah Qaf a wata tattaunawa ta wayar tarho da shirin Duniya wa Din. Hakan ya sanya mai gabatarwa da bakon kwararre na shirin tunani kuma ya samu tarba daga masu sauraron wannan shirin.