IQNA

Kocin kwallon kafa a Faransa ya musunta gargin kiyayya da musulunci da ake yi masa

15:53 - December 17, 2023
Lambar Labari: 3490326
Tsohon kocin kulob din Nice na Faransa ya musanta zargin da ake masa na yada kiyayya ga Musulunci.

A cewar Al-Arabi Al-Jadeed, Christophe Gaultier, tsohon kociyan kulob din na Nice, ya bayyana a gaban kotun birnin Nice domin kare kansa daga tuhumar da ake masa dangane da ayyukan wariya da yada kiyayya ga Musulunci.

A wannan zaman, alkalin ya saurari bayanai da kuma kare-karen Galatier sannan ya bayyana ranar yanke hukuncin karshe a ranar 21 ga watan Disamba.

Shafin yanar gizo na gidan rediyon Faransa RMC Sport ne ya wallafa cikakken bayanin zaman, inda wanda ake tuhumar ya halarta tun da sanyin safiya.

Idan har aka tabbatar da tuhume-tuhumen a kan wannan kocin na Faransa zai fuskanci hukunci mai tsanani, wanda zai kai shekaru uku a gidan yari da kuma tarar Yuro 45,000.

Mai gabatar da kara ya bukaci a ba wa wannan kocin Faransa hukuncin zaman gidan yari na shekara daya tare da biyan tarar Yuro 45,000 da kuma dakatarwa ta shekaru 3 daga harkokin kwallon kafa.

Ana zargin Christon Gaultier da mayar da martani mara kyau game da azumin da ‘yan wasa Musulmi na kungiyarsa suka yi da kuma yin kalamai na kin jinin Musulunci. Ko da yake ya yi ikirarin a gaban kotun cewa ya damu ne kawai game da lafiyar 'yan wasan kungiyarsa wadanda suka daina ci da sha na sa'o'i saboda azumi da kuma shiga wasannin kwallon kafa.

 

 

 

4188363

 

captcha