IQNA

Zanga-zangar Musulmin kasar Thailand na nuna goyon bayan Falasdinu

16:14 - December 22, 2023
Lambar Labari: 3490347
Bankok (IQNA) Al'ummar Musulman yankin Patani na kasar Thailand sun bayyana goyon bayansu ga Falasdinu tare da neman kawo karshen yakin tare da yin Allah wadai da laifukan da gwamnatin sahyoniya ta aikata a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, al’ummar musulmin yankin Pattani na kasar Thailand a yayin jerin gwanon da suka shirya tun daga tsakiyar birnin zuwa cibiyar musulunci na wannan birni, sun bukaci da a kawo karshen yakin da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi kan al’ummar Palastinu da ake zalunta.

A cikin bayanin karshe na wannan tattakin, an sanar da cewa: Abin da muke gani yana faruwa a Gaza a yanzu laifuffuka ne na cin zarafin bil adama. Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta katse ruwan sha, wutar lantarki da abinci ga wadannan mutane, kuma mu musulmin kasar Thailand muna adawa da duk wadannan laifuka, kuma duk wanda bai ji haushin wadannan abubuwan ba, to ya yi shakku kan yadda yake ji na dan Adam.

4189278

 

captcha