IQNA

Cikakkun bayanai kan gasar zaben kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Mauritaniya

22:01 - February 14, 2024
Lambar Labari: 3490635
IQNA - A jiya 23 ga watan Fabrairu ne aka fara gudanar da gasar kur’ani ta kasar Mauritaniya, da nufin zabar wakilan wannan kasa da za su halarci gasar kur’ani ta kasa da kasa a kasashe daban-daban na duniya.

Kamar yadda Iqna ta ruwaito; Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na "Nowakshout News" cewa, ana gudanar da wadannan gasa ne bisa kokarin ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Mauritaniya da nufin zabar wakilan wannan kasa da za su halarci gasar kur'ani ta kasa da kasa a kasashen duniya daban-daban.

A gasar ta bana, akwai mahalarta 500, wadanda kusan 90 ke cikin rukunin mata.

Al-Dah Wold Sidi Wold Amer Taleb, ministan harkokin addinin musulunci da ilimi na kasar Mauritaniya, a jawabin da ya gabatar a wajen bude wannan gasa, ya yaba da irin dimbin halartar wannan gasa idan aka kwatanta da na baya.

Daga nan sai ya yaba da irin yadda mata suke shiga wannan gasa inda ya ce: Ana gudanar da wadannan gasa ne da nufin zabar wakilan kasar Mauritaniya da za su shiga gasar kur'ani ta kasa da kasa kamar Dubai, Malaysia, Kenya, Kuwait da dai sauransu.

A cewar ministan harkokin addinin muslunci na kasar Mauritaniya, wannan gasa tana taka rawa a kusa da gasar haddar da fahimtar litattafan addinin muslunci ta kasa mai suna "Award President".

A nasa bangaren shugaban alkalan gasar Wold Seyed al-Haj ya bayar da tabbacin gudanar da gasar ga dukkan mahalarta gasar tare da jaddada muhimmiyar rawar da wannan gasar ke takawa wajen ilmantar da kur’ani da iliminta.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4199624

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ilimi gasa kur’ani jaddada mahalarta
captcha