Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, da tawagar da suke tare da su sun rasa rayukansu bayan da jirgin helikwaftan da ke dauke da su ya yi hadari a lardin Gabashin Azarbaijan da ke arewa maso yammacin kasar saboda tsananin yanayi a ranar Lahadi.
An gano gawarwakin nasu ne a ranar Litinin bayan wani gagarumin bincike da aka yi cikin dare.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sakon ta'aziyya a yau Litinin, inda ya bayyana zaman makoki na kwanaki biyar. Za a gudanar da jana'izar ne a garuruwa da dama daga ranar Talata zuwa Alhamis.