IQNA

Marigayi Ministan Harkokin Waje Hossein Amir-Abdollahian: Takaitaccen Tarihin Rayuwa

IQNA – Marigayi ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayu, 2024, tare da shugaban kasar Ebrahim Raisi.

Tawagar dai tana dawowa ne daga bikin bude madatsar ruwa ta hadin gwiwa da jamhuriyar Azabaijan a lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi hadari a tsaunukan Varzaghan na lardin Azarbaijan ta gabas.

Abin da ke tafe shi ne takaitaccen tarihin jami'in diflomasiyyar Iran.