Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Sheikh Abu Bakr bin Zubair bin Ali babban mufti na kasar Tanzaniya ya bayyana cewa, shahadar Ayatullah Ibrahim Raisi, shahidi Amir Abdullahian da sauran shahidai, labari mai cike da tashin hankali da sanya bakin ciki, sannan a sa'i daya kuma, ya isar da sakon ta'aziyyar wannan lamari a madadinsa da na musulmin kasar Tanzaniya, ya mika ta'aziyyarsa ga jakadan Iran a Tanzaniya, da shugabanni da al'ummar Iran.
Ya kuma halarci ofishin jakadancin kasar Iran domin jajantawa tare da sanya hannu kan littafin tunawa da shahidan.
Har ila yau babban Mufti na kasar Tanzaniya ya gudanar da sallar jana'izar a babban masallacin sa kwana guda bayan binne gawar shahidan.
An gudanar da wannan addu'a ne a masallacin mufti tare da halartar ma'abota addini, da kuma wakilin ofishin jakadancin kasar Iran.