IQNA

Ganawar da jakadan Iran a Saudiyya ya yi da shugaban majalisar koli ta alhazai ta Saudiyya

14:55 - May 27, 2024
Lambar Labari: 3491229
IQNA - Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Saudiyya ya gana da Abdulaziz bin Saud bin Nayef, ministan harkokin cikin gida kuma shugaban majalisar koli ta alhazai ta Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Alireza Enaiti, jakadan jamhuriyar musulinci ta Iran a kasar Saudiyya ya gana tare da tattaunawa da Abdul Aziz bin Saud bin Nayef ministan harkokin cikin gida kuma shugaban majalisar koli ta alhazai ta kasar Saudiyya.

A farkon wannan taron, ministan harkokin cikin gida na kasar Saudiyya ya bayyana alhininsa game da shahadar Ayatullah Ibrahim Raisi da Dakta Hossein Amirabdollahian da tawagar da ke tare da shi, tare da fatan lafiya da nasara ga gwamnati da al'ummar Iran.

Jakadan na kasarmu ya kuma mika godiyarsa ga mahukuntan kasar Saudiyya bisa aikewa da sakon ta'aziyya, kiran waya da aika tawaga zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cikin wannan taron, Enayati ya bayyana aikin Hajji a matsayin wurin haduwar musulmi kuma wata alama ce ta hadin kan Musulunci tare da jaddada hadin kai da hadin gwiwar kasashen biyu wajen gudanar da aikin Hajji lafiya.

Ministan harkokin cikin gida na Saudiyya ya ce kasarsa ta dauki dukkan matakai na gudanar da aikin Hajji a kai a kai da kuma dawowa lafiya.

 

 
 

4218541

 

 

 

 

 

 

 

captcha