IQNA

Shirin Ma'aikatar kula da harkokin addini ta Masar na fadada ayyukan gidan rediyon kur'ani

15:36 - May 28, 2024
Lambar Labari: 3491237
IQNA - A jawabin da ya gabatar a zauren majalisar dokokin kasar Masar Mohammed Mokhtar Juma, ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ya bayyana shirin ma'aikatar na fadada ayyukan gidan rediyon kur'ani na birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Masri Al-Youm cewa, a jiya litinin Mohamed Mokhtar Juma, ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar, a lokacin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin kasar, yayin da yake sanar da hakan ya bayyana cewa: Tare da hadin gwiwar kafafen yada labarai na kasar Masar, an shirya tsarin fasaha da ci gaban bil'adama na gidan rediyon kur'ani a birnin Alkahira kuma ana kan aiwatar da aikin; A karon farko tun bayan kafa gidan radiyon kur'ani mai tsarki na birnin Alkahira, za a dauki sabbin masu karatun kur'ani goma sha biyu da za su yi karatu a rediyo.

Mohammad Mukhtar Juma ya jaddada cewa: Shekaru goma da suka gabata a kasar Masar za a iya tuna zamanin gyaran masallatai, to an  dawo da su, da kuma fadada ayyukan kur'ani a kasar. A cikin wannan lokaci an gyara masallatai sama da 12,000 da suka hada da masallacin Imam Hussain (AS) da Sayyida Zainab (S) da Masallacin Sayyida Nafisa da sauran masallatai na tarihi da dama da aka kashe sama da fam biliyan 18 na kasar Masar.

A cewar ministan, an kuma fadada kewayen masallatan domin halartar masallata da kuma masu ziyara.

Dangane da bukatar daya daga cikin wakilan cibiyar bunkasa harkokin kur'ani da tarbiya a masallatai, ya ce: Yanzu haka sama da da'irar kur'ani dubu 7 ne ke aiki a masallatan kasar Masar, a daya bangaren kuma, da'irar kur'ani na musamman na kananan yara da mata su ma an kafa su kuma sun  sami karbuwa sosai.

 

4218809

 

 

 

 

 

 

captcha