IQNA

An fitar da sabbin bayanai na gina masallacin karkashin ruwa na farko a duniya a Dubai

16:00 - June 04, 2024
Lambar Labari: 3491279
IQNA - Nan ba da dadewa ba ne za a fara aikin ginin masallacin karkashin ruwa na farko a duniya a birnin Dubai kuma ana sa ran za a kashe dala miliyan 15 domin gina wannan masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sashen kula da harkokin addinin muslunci da ayyukan jin kai na birnin Dubai (IACAD) ya sanar da cewa nan ba da dadewa ba za a fara aikin gina masallacin karkashin ruwa na farko a duniya a wannan masarauta.

Wannan masallacin zai kasance na farko da aka gina irin wannan a duniya da ke da gine-gine na musamman kuma zai kasance yana da hawa uku. A Hotunan da aka buga na shirye-shiryen wannan masallaci, rabin wannan ginin zai kasance a saman ruwa, tare da wuraren zama da kantin kofi, yayin da sauran rabin, ciki har da zauren da ake amfani da shi a matsayin gidan sallah, zai kasance a karkashin ruwa.

Wannan masallacin zai dauki nauyin masallata kusan 50 zuwa 75 wadanda za su samu kwarewa ta musamman na yin addu'o'i a karkashin ruwa. Wannan ginin da ya nutse kuma zai kasance da alwala da bandaki. Masu ginin sun kiyasta cewa za a kashe dala miliyan 14.9 don gina wannan aikin.

An bayyana shirye-shiryen wannan masallaci a yayin da sashen kula da harkokin addinin musulunci da ayyukan agaji na Dubai suka gudanar da taro kan wannan aikin yawon bude ido na addini.

Ahmed al-Mansouri memba na wannan kungiya ya ce nan ba da jimawa ba za a fara aikin gina wannan masallaci a Dubai, amma har yanzu ba a tantance ainihin wurin da masallacin zai kasance ba.

Al-Mansouri ya ce: Wannan masallacin zai kasance kusa da gabar teku sosai, kuma masu ibada za su iya shiga wannan masallaci ta wata gada da ke hade da kasa.

Ya ce masallacin zai kasance a bude ga ma’abota kowane irin addini, amma za a bukaci maziyartan su sanya tufafi masu kyau da kuma kiyaye al’adu da al’adun Musulunci.

 

4219882

 

 

captcha