IQNA

Mahajjatan Iran sun Karanta Addur’ar Kumail a Makka

18:33 - June 07, 2024
Lambar Labari: 3491296
IQNA - A daren jiya ne aka gudanar da taron  karatun addu’ar Du’aul Kumail a birnin Makka mai alfarma tare da halartar dubban mahajjata na kasar Iran.

Kamar yadda Iqna ta ruwaito; An gudanar da taron karatun  addu’ar Du’aul Kumail a otal-otal da ayarin  Iran ke sauka a birnin Makka, kuma dubun dubatar alhazan Iran da ke kusa da Baitullahi Al-Haram a daren ranar Alhamis, sun halarci wanna taron addu’a.

An gudanar da taron karatun addu’ar Du’aul Kumail a Makkah a wannan mako a Meydan Kadi Tower 2 da Al-Balad Al-Tayeb hotels  da sauran otal-otal da mahajjata ke sauka a wannan kasa ba tare da bata lokaci ba da kuma a ci gaba da gudanar da ayyukan ibada.

A wajen taron a otel na "Violet" wanda ya samu halartar Hujjatul-Islam Sayyid Abd al-Fattah Nawab, wakilin Waliyul Faqih a al'amuran hajji da umrah; Sayyid Abbas Hosseini, shugaban hukumar Hajji da Umrah  da kuma jami'an tawagar Jagora da na hukumar Hajji da kuma jagoran mahajjatan Iran, sun yi bayani kan ayyukan da Imam Javad (a.s.) ya bayar a lokutan rabin farko na watan Zul-Hijja kuma ya fayyace ta hanyar kawo ayoyi da hadisai: Ya kamata mutum ya kasance yana da alaka da muminai da kuma nisantar karkata ga makiya Musulunci.

Har ila yau, an gudanar da taron karatun addu’ar Du’aul Kumail a otal din Meydan Shahr da ke birnin Makkah, tare da jawabin Hojjatul Islam Heidari Kashani, daya daga cikin masu gabatar da wa'azi, da kuma Hamid Ramadanpour mai wakokin yabo na Ahlul bait (AS)

A cikin wannan taro, Hojjatul Islam Heydari Kashani ya yi bayani kan matakan godiya da alamomin aikin Hajji Maqboul.

 

4220196

 

 

captcha