IQNA

Al-Azhar: Shirun da duniya ta yi kan zaluncin yaduwan sahyoniya da kisan kiyashin da suke yi bai halatta ba

15:11 - June 09, 2024
Lambar Labari: 3491308
IQNA - Cibiyar Musulunci ta Al-Azhar ta kasar Masar, dangane da kisan da aka yi wa daruruwan Falasdinawa a garin Nusirat na zirin Gaza, wanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi a jiya, ta sanar da cewa: Shirun da duniya ta yi kan cin zalun da yahudawan sahyoniyawan suke yi abu ne da ba za a amince da shi ba. kuma wannan laifi tabo ne ga bil'adama.

cibiyar Al-Azhar ta kasar Masar da ake yi wa kallon a matsayin babbar cibiya ta muslunci a wannan kasa, ta fitar da ke a matsayin martani ga kisan gillar da aka yi wa Palastinawa a yankin Al-Nusirat  sansani a zirin Gaza.
A cikin sanarwar da ta fitar, Al-Azhar ta dauki kisan gillar da aka yi wa fararen hula Falasdinawa da dama a Nusirat a matsayin wani laifi na dabbanci, ta kuma ce 'yan ta'adda yahudawa na  haramtacciyar kasar Isra'ila sun aikata ayyukan barna  da kuma zalunci.
Cibiyar a cikin bayaninta ta bayyana cewa: Kisan da aka  yi, ya yi  sanadin mutuwar mutane sama da dari biyu da kuma jikkata daruruwan mutane, wanda hakan  wani sabon laifi ne da ya kara dagula tarihin gwamnatin sahyoniyawan kan Palastinawa wadanda su ne suke da kasar.
A yayin da take yin Allah wadai da laifukan dabbanci na gwamnatin sahyoniyawan, Al-Azhar ta bukaci al'ummomin kasa da kasa da masu zaman kansu da su dakatar da zubar da jinin da ake yi a Gaza da kuma tallafa wa fararen hula da suka hada da mata da yara da kuma tsofaffi, tare da hukunta gwamnatin sahyoniyawan da take hakkinsu, da yin watsi da dokokin kasa da kasa, domin yinshiru kan laifukan 'yan ta'addan sahyoniyawa, babban tabo ne a goshin dukkanin al’ummomin duniya, wanda tarihi ba zai manta da hakan ba.
Ita dai wannan cibiya ta Musulunci ta Masar ta dauki mummunan yanayi da rashin mutuntaka a Gaza a matsayin sakamakon goyon bayan wasu gwamnatoci da suke baiwa Isra’ila, inda ta ce: Ana aiwatar da kisan kiyashi a Gaza tare da goyon bayan wasu gwamnatoci dari bisa dari.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar Al-Azhar ta kasar Masar da ake yi wa kallon a matsayin babbar cibiya ta muslunci a wannan kasa, ta fitar da ke a matsayin martani ga kisan gillar da aka yi wa Palastinawa a yankin Al-Nusirat  sansani a zirin Gaza.

4220495

captcha