IQNA

Mahajjata sun ziyarci cibiyar sarki Fahd inda ake buga kur'ani

15:10 - June 22, 2024
Lambar Labari: 3491382
IQNA - Sama da alhazai maza da mata dubu uku ne daga kasashe 88 na duniya suka ziyarci cibiyar sarki Fahad da ke buga kur’ani mai tsarki a lokacin aikin hajjin bana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Riyadh cewa, sama da mahajjata maza da mata dubu uku daga kasashe 88 na duniya ne suka ziyarci cibiyar sarki Fahad da ke  buga kur’ani mai tsarki a lokacin aikin hajjin bana.

An gudanar da wannan taro ne a wani bangare na shirin "Bakin Rahman" na ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci, da'awah da jagoranci ta kasar Saudiyya.

A ziyarar da suka kai cibiyar buga kur’ani mai tsarki mafi girma a duniya, bakin sun fahimci matakai daban-daban na bugu da tarjama kur’ani mai tsarki, tun daga farkon matakin rubuta kur’ani har zuwa karshen bita da kuma daidaita rubuce-rubucen. da kuma fassararsa zuwa harsuna daban-daban da kuma rarraba su a tsakanin musulmin duniya.

A karshen wannan ziyarar, cibiyar buga kur’ani mai tsarki ta Sarki Fahd, ta bayar kyautuka na kwafin kur’ani mai tsarki tare da tarjamarsa cikin harsuna daban-daban ga mahajjata.

 

 

4222544

 

 

 

 

captcha