IQNA

Baje kolin Ghadir a hubbaren Sayyida Ma’asumah

16:00 - June 22, 2024
Lambar Labari: 3491386
IQNA - An gudanar da baje kolin Ghadir a cikin rumfuna daban-daban masu ban sha'awa a farfajiyar hubbaren Sayyida Ma’asumah a daidai lokacin idin Imamanci da Wilaya ke kara gabatowa (a.s.).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren Ma’asumah (AS) cewa, bikin baje kolin idin Ghadir na farawar shekarun imamanci da wilaya ya fara ne tun daga idin al-Adha kuma zai ci gaba har zuwa ranar 20 ga watan Zul-Hijjah a hubbaren Sayyida Fatima Masumah.

Wannan baje kolin ana bude shi ga masu ziyara a kowace rana daga 19:00 zuwa 23:00 a cikin farfajiyar hubbaren Sayyida Fatima Ma’asumah Amincin Allah ya tabbata a gare ta.

Abin tuni shi ne cewa, ta hanyar halartar wannan baje kolin, maziyartan za su iya ziyartar wuraren da aka kebe domin nuna surar Ghadir Khum tare da bayar da labarin waki'ar Ghadir.

Sannan kuma an ware wurin shakatawa na yara, rumfar rubutu, tambayoyin Shari'a da wurin daukar hoto na yara.

 

4222611

 

 

 

 

captcha