Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren Imam Husaini (AS) Ali Kazem Sultan shugaban cibiyar gudanar da bukukuwa na Ahlulbaiti (AS) a hubbaren ya ce: A daidai lokacin gabatowar Idin Ghadir Khum, cibiyar hubbaren Haramin Imam Hussain (AS) za ta gudanar da bikin na tsawon kwanaki uku, wanda zai fara a gobe litinin 24 ga watan Yuli.
Ya kara da cewa: Wannan biki ya hada da ziyarar jami'an wasu hukumomin gwamnati domin taya hubbaren Hosseini murna, tare da daga tutar Idin Ghadir a daren Ghadir, da gudanar da dararen wake-wake da kuma gabatar da shirin Tawashih a wuraren ibada.
Shi ma wannan jami'in kula da harkokin al'adu na hubbaren Imam Hussain (AS) ya ce: Har ila yau wannan biki ya hada da wadanda za a gudanar a wasu lardunan da ke wajen Karbala da raba kyaututtuka ga wadanda suka nuna wazo wajen gabatar da kasidu da wakokin yabon ahlul baiti.
Za a rufe harabar Haramin Imam Husaini (AS) da korayen kyallaye na Idin Ghadir.