IQNA

Jagoran juyin Musulunci ya kada kuri'arsa

16:23 - June 28, 2024
Lambar Labari: 3491418
IQNA - Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya kada kuri'arsa a cikin mintuna na farko na zaben shugaban kasar karo na 14.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kada kuri’arsa ne a mintunan farko na fara kada kuri’ar zaben shugaban kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran karo na 14, inda ya halarci rumfar zabe ta 110 a Husainiyar Imam Khumaini.

Fiye da 'yan jarida 200 daga kafofin watsa labarai na cikin gida da na waje, ciki har da 'yan jaridu daga Amurka, Sin, Rasha, Jamus, Spain, Ingila, Afghanistan, Austria, Turkey, Kuwait, Netherlands, UAE, Italiya, Iraki, Yemen, Japan, Faransa, Philippines, Lebanon , Qatar, Oman, Australia, Sweden, Denmark, India, Koriya ta Kudu da sauransu suna bayar da rahotanni kan zaben.

Idan dai ba a manta ba a ranar Juma’a 8 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben shugaban kasa karo na 14, wanda ya kamata a gudanar da shi a watan Yunin shekara mai zuwa, bayan shahadar shugaba Ayatollah Raisi da tawagarsa.

4223328

 

 

 

 

captcha