Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana gudanar da tarurrukan Anas da kur’ani mai tsarki musamman ga mahajjatan Madina a otal din da alhazan Iran suke sauka.
Sayyid Reza Najibi, fitaccen makaranci kuma memba a ayarin kur’ani mai suna “Noor” ya karanta ayoyi daga Kalmar Allah a wajen taron Anas da kur’ani mai tsarki, musamman ga mahajjatan Ahlus-Sunnah a Madina Munura.
An gudanar da wannan taro na kur'ani ne da yammacin ranar Asabar 6 ga watan Yuli a otal din "Araek Tayyaba", kuma gungun 'yan uwa 'yan Sunna daga lardin Sistan da Baluchistan ne suka halarci wannan taro.