Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, ma’aikatar harkokin cikin gidan gwamnatin Khalifa a kasar Bahrain ta hana Sheikh Saleh Al-Ibrahim zuwa kan minbari tare da bayyana cewa shi ba Bahraini ba ne wajen kafa hujja da hakan.
A baya dai ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Bahrain ta gayyaci shugaban kwamitin zaman makoki na yankin Al Deir domin rera taken yin Allah wadai da gwamnatin sahyoniyawan da magoya bayanta a yayin gudanar da zaman makoki da kuma gudanar da jerin gwano a wannan yanki.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta tilasta masa sanya hannu kan wata takarda da ta haramta yin irin wadannan take.
A yammacin ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli, 2024, jami'an tsaro sun kama wasu mutane 5 a kauyen Aali yayin da suke halartar taron tunawa da Ashura.
Irin wadannan ayyuka wani bangare ne na ci gaba da cin zarafi na zalunci da gwamnatin Bahrain take yi kan 'yan kasar da ke halartar wannan taro.
https://iqna.ir/fa/news/4226790/