Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Alam cewa, majalisar lardin Karbala ta sanar a jiya Alhamis cewa kimanin masu ziyara miliyan 6 ne daga kasar Iraki da sauran kasashen duniya suka halarci tarukan Ashura a birnin Karbala.
Bangaren yada labarai na wannan majalissar ya kara da cewa adadin masu ziyara na wannan shekara na Ashura da zaman makokin Taweerij a Karbala ya kai kimanin mutane miliyan shida.
Kafin nan dai ma’aikata, da jami’an tsaro da na kiwon lafiya sun sanar da nasarar shirin na musamman na tarukan Ashura da makokin Taweerij.
Hukumar yada labarai da sadarwa ta kasar Iraki ta sanar da cewa, 'yan jarida 725 da tashohin tauraron dan adam 84 ne suka halarci tarukan Ashura.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar wutar lantarki ta kasar Iraki ta fitar, ta bayyana shirin na musamman na Taron Ashura da samar da wutar lantarki na sa'o'i 24 a birnin na Karbala a matsayin nasara.
Har ila yau filin jirgin saman Najaf Ashraf ya sanar da karbar bakuncin masu ziyara sama da dubu 71 daga ranar 1 zuwa 9 ga watan Muharram.