Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mabiya mazhabar shi’a da iyalan gidan manzon Allah (SAW) a birnin San Jose sun halarci cibiyar musulunci ta Saba a matsayin daya daga cikin manyan cibiyoyi na addinin muslunci na mabiya mazhabar shi’a a Amurka domin gudanar da tarukan tunawa da shahadar Imam Husaini (a.s).
Har ila yau, yara sun yi jimamin tuta na hubbaren Sayyid Al-Shohada (AS) a cikin Husseiniyyah mai albarka.
Saba Islamic Center daya daga cikin cibiyoyin Musulunci a San Jose, California, Amurka. An kafa wannan cibiya a shekarar 1979 kuma ta ci gaba da ayyukanta na addini da na al'adu har zuwa yanzu.