Kamfanin dillancin labaran ya habarta cewa, masu zanga-zangar sun daga tutocin Falasdinu da na kungiyar Hamas tare da rera taken nuna goyon baya da kuma goyon bayan Palastinu da guguwar Al-Aqsa.
An fara samun ci gaba a shawarwarin tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Hamas a 'yan watannin nan, kuma Biden da manyan jami'an tsaron kasar sun shiga tsakani a kokarin cimma matsaya.