IQNA

Paparoma ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a Gaza

13:38 - August 08, 2024
Lambar Labari: 3491660
IQNA - Shugaban kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis a lokacin da yake jawabi ga jama'a a fadar Vatican, ya yi nuni da mummunan halin jin kai da ake ciki a zirin Gaza tare da yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a wannan yanki.

A cewar tashar Al-Alam, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya a yayin wannan jawabi ya jaddada cewa idan muka dogara ga Allah, za mu shaida abubuwan al'ajabi.

A ci gaba da jawabin nasa, yayin da yake ishara da dimbin tashe-tashen hankula da ake ta fama da su a halin yanzu a dukkanin sassan duniya, ya ce: Na yi bakin ciki kan dukkan tashe-tashen hankulan da ake fama da su a sassan duniya, musamman a Gaza, inda ‘yan adan suke cikin matukar wahala kuma ba zai yiwu a kauda kai daga hakan ba,  ina rokon su da su tsagaita wuta domin shimfida hanyar samar da zaman lafiya.
Fafaroma Francis ya kuma bukaci al'ummar duniya da su yi addu'ar samun nasarar soyayya a kan kiyayya da kwance damarar daukar fansa tare da gafara, sannan ya jaddada cewa: Ina fatan al'ummar kasashe irin su Ukraine, Myanmar da Sudan, wadanda suka jure wa wahalhalun yaki nan ba da jimawa ba za a samu zaman lafiya mai dorewa. 
A yayin jawabin nasa, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya kuma yi kira da a kawar da wariya, musamman ga mata a kasashe irin su Pakistan da Afghanistan.

 

4230719

 

 

captcha