A rahoton Al Jazeera; Sama da mutane dari ne suka yi shahada a wannan harin bam da ya faru a lokacin sallar jam'i da al'ummar Palasdinu suka yi a wata makaranta da ke tsakiyar birnin Gaza.
A cewar wannan rahoto, an kuma jikkata wasu mutane da dama a wannan harin.
Kafofin yada labaran Falasdinu sun sanar da cewa, hare-haren da mayakan haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan wannan makaranta da ke unguwar al-Darj a tsakiyar birnin Gaza ya faru ne a lokacin da wani gungun Palasdinawa ke gudanar da sallar asuba a can.
Sojojin Isra'ila sun fitar da wata sanarwa a baya-bayan nan inda suka yi iƙirarin cewa "sun kai hari ga masu zagon ƙasa da ke aiki a cikin wannan makaranta."
Sanarwar da sojojin yahudawan sahyuniya suka fitar na cewa: Sojojin Hamas na amfani da wannan makaranta wajen fakewa da kai hare-hare iri-iri kan sojoji da dakarun gwamnati.
A karshen sanarwar da ta fitar, sojojin Isra'ila sun zargi Hamas da keta dokokin kasa da kasa.