A rahoton shafin jaridar al-Ghad, Muhammad Abu Saadah mai wa'azi kuma limamin majami'ar Gaza wanda ya yi shahada a safiyar yau a harin bam da aka kai a makarantar Al-Darj yana karanta wadannan ayoyi na suratul Zakhraf a cikin wannan faifan bidiyo:
A ranar Asabar din da ta gabata ce mayakan yahudawan sahyuniya suka kai farmaki kan masallacin makarantar Taba'een da ke unguwar al-Darj a birnin Gaza a lokacin sallar asuba, lamarin da ya yi sanadin shahadar Palasdinawa akalla 100 tare da jikkata wasu daruruwan na daban.
A yayin da sojojin yahudawan sahyoniya suka yi ikirarin cewa wannan makaranta da ke zirin Gaza hedikwatar dakarun Hamas ce, mafi yawan shahidan wannan mummunan aika-aikar da gwamnatin sahyoniyawan ta yi a wannan makaranta yara ne da tsoffi.
A cewar wannan rahoto, wannan makaranta ta kasance wurin zama na ‘yan gudun hijirar Falasdinu.