Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Kafil cewa, Mohannad Al-Miyali, daraktan cibiyar kur'ani mai tsarki mai alaka da majalisar ilimin kur'ani a hubbaren Abbasi ne ya sanar da hakan inda ya ce: Wannan shiri na musamman ne ga maziyarta da suka ziyarci Imam a Haramin Husaini a lokacin aikin ziyara na Arbaeen (a.s) da Sayyidina Abbas (a.s) . A cewarsa, wannan aiki na daya daga cikin tsare-tsare da ke da nufin karfafawa da inganta harkokin kur'ani a tsakanin yara da matasa.
Ya kara da cewa: Wannan shiri ana gudanar da shi ne karo na hudu a jere, wanda ya hada da ayyuka da dama na mu’amala da ilmantarwa da suka hada da gasar kur’ani mai tsarki da laccoci na ilmantarwa, wanda ke da nufin inganta ayyukan addini da na kur’ani a tsakanin matasa masu ziyara.
Bugu da kari, a bisa fadada ayyukan kur'ani mai tsarki, majalissar ilmin kur'ani mai tsarki ta hubbaren Abbasi ta bude tashar farko ta shirin horas da maziyarta a karbala.
A cewar Jawad Al-Nasrawi daya daga cikin jami’an wannan majalissar, an bude wannan aiki ne a hanyar masu ziyarar Arbaeen a Maafal Babol, kuma manufarsa ita ce karantar da sahihin karatun kur’ani mai tsarki ga masu ziyarar Arbaeen.
Ya kara da cewa: Shirin bayar da horon karatun kur'ani ya hada da tashoshi 8 na tsakiya da na ilimi a lardin Karbala, wadanda ke cikin Karbala da suka hada da na Bagadaza, Babila, Najaf da Ain al-Tamar.
Al-Nasrawi ya kara da cewa: Wannan shiri ya hada da koyar da sahihin karatun suratu Fatiha da gajerun surori ga masu ziyarar Arbaeen, da gudanar da da'irar kur'ani, da gasar koyon karatu da kuma halartar matasa masu haddar kur'ani mai tsarki.