A rahoton al-Quds al-Arabi, masallacin Aqaba Bin Nafe, daya daga cikin tsofaffin masallatai a Afirka, ya shaida irin ayyukan da ake gudanarwa duk shekara domin tunawa da maulidin Manzon Allah (SAW).
A bana daruruwan mutane daga ciki da wajen kasar Tunisia ne suka halarci bikin maulidin manzon Allah (SAW), wanda aka gudanar a masallacin "Aqba bin Nafi". An gina wannan masallaci a shekara ta 50 bayan hijira, kuma ana daukarsa daya daga cikin masallatai na farko da musulmi suka gina a arewacin Afirka.
Idan dai ba a manta ba a duk fadin duniya ne musulmi ‘yan Sunna a fadin duniya suke gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) a kowace shekara a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal. Kasashe da dama na musulmi da al'ummar musulmi sun shaida bukukuwa da ayyuka daban-daban na tunawa da wannan lokaci.