Bukin bude gasar kur'ani ta kasa da kasa ta Malaysia karo na 64
An fara bikin bude gasar kur'ani ta kasa da kasa ta Malaysia karo na 64 da jawabin firaministan kasar. A cikin wannan zagayen gasar, mahalarta 92 daga kasashe 71 na duniya ne suka halarci bangarorin biyu na haddar kur’ani mai tsarki.