IQNA

Shugaban kasar Tunisia:

Tunisiya ba ta neman daidaita alaka da gwamnatin yahudawan sahyoniya

16:28 - October 22, 2024
Lambar Labari: 3492073
IQNA - Shugaban kasar Tunusiya yayin da yake rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar a majalisar dokokin kasar, ya jaddada cewa kasarsa ba ta neman daidaita alaka da gwamnatin Harmtacciyar kasar Isra'ila.

A cewar jaridar Arabi 21, shugaban kasar Tunusiya Qais Said ya yi rantsuwar kama aiki a majalisar dokokin kasar a karo na biyu a hukumance.

A cikin jawabin nasa ya bayyana kalubalen da kasarsa ke fuskanta a fannin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, sannan kuma ya jaddada cewa kwata-kwata ba shi da niyyar daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawa.

A ranar 11 ga watan Oktoban wannan shekara, Farooq Buaskar, shugaban zabe mai zaman kanta da ke shirya zabe, ya sanar da cewa, Qais Saeed ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Oktoban 2024 da samun kashi 90.69% na kuri'un da aka kada.

Qais Saeed ya ce a bikin kaddamar da aikin nasa: Babban kalubalen da za a ci gaba da fuskanta gadan-gadan shi ne bude wata sabuwar hanya ga marasa aikin yi, musamman matasa.

Ya yi nuni da cewa, akwai kalubale da dama da ya kamata a gaggauta shawo kan su, wanda na farko shi ne tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da cin hanci da rashawa, kuma ana ci gaba da kulla makarkashiyar da ta kai kasar cikin rudani.

Shugaban kasar Tunusiya ya bayyana cewa, ko kadan ba mu da niyyar daidaita alaka da gwamnatin yahudawan sahyoniya, ya ce: Ba mu da wata kalma da ake kira daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan masu cin zarafi da aikata muggan laifuka, kuma duk wani mai mu'amala da wannan gwamnatin ya aikata laifin cin amanar kasa ga Falasdinu.

Qais Saadi ya bayyana cikakken goyon bayansa ga al'ummar Palastinu tare da jaddada yin Allah wadai da kisan kiyashin da gwamnatin Sahayoniyya ke yi tare da jaddada goyon bayansa ga al'ummar kasar Labanon.

 

4243660

 

 

 

 

captcha