Iran ba za ta yi watsi da hakkinta na mayar da martani kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba, Wannan wani hakki ne kuma wani nauyi ne na gwamnati, don haka, muna da niyya ta gaske wajen mayar da martani,”in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei a taron manema labarai na mako-mako a wannan Litinin.
Da sanyin safiyar Asabar ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai hari kan wasu cibiyoyin sojin Iran, inda suka kashe jami'an soji hudu da farar hula guda.
Bangaren soji masu tsaron sararin samaniya na Iran ya ce an samu barna kadan a wasu yankuna, inda ake gudanar da bincike kan girman su da kuma martanin da ya dace da hakan.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya fada a ranar Lahadi cewa Iran ba ta neman yaki amma za ta bayar da darasin da ya dace game da sabon matakin wuce gona da iri na Isra'ila.
Baghaei ya ce, tofin Allah tsine kan keta hurumin kasar Iran da Isra'ila ta yi, daga bangaren kasashen yankin da ma sauran kasashen duniya, ya kara tabbatar da matsaya ta kasashen duniya akan ayyukan barna da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aikatawa.
Ya ce; Baki ya zo daya a tsakanin Kasashen yankin kan cewa, mamayar da gwamnatin Sahayoniya ta shafe shekaru 80 tana ayi a kan yankunan Falastinu ita ce babbar matsala kuma tushen rashin tsaro a yankin
Kakakin na Iran ya jaddada cewa, kasashen yankin sun dorawa magoya bayan Isra'ila alhakin hana kungiyoyin kasa da kasa, musamman ma kwamitin sulhu na MDD daukar duk wani mataki da ya dace a kan laifukan yake da keta alfarmar kasashe da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa babu wata kasa makwabciyar Iran da zata bar Isra’ila ta yi amfani da yankinta wajen kai hari a kan Iran.