IQNA

A gefen taron ganawa da dalibai;

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ziyarci baje kolin ayyukan matasa masu fasaha

14:13 - November 04, 2024
Lambar Labari: 3492147
IQNA - Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci baje kolin ayyukan matasa masu fasaha a gefen taron daliban a jiya.

Shafin  yanar gizo na ofishin kiyayewa da yada ayyukan Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya habarta cewa, a gefen taron dalibai na ranar asabar 12 ga watan Nuwamba, jagoran juyin juya halin Musulunci ya ziyarci zane-zane na daliban da suke halartar bikin. Kamfen na "Akhrashe" da tattaunawa da wasu daga cikin wadannan matasa masu fasaha.

Wannan yunkuri na "Akhrashe" shi ne mayar da martani da ma'anar alhakin dalibai masu zane-zane game da bala'o'i a Gaza. A cikin wannan aikin, ɗalibai matasa masu fasaha fiye da dubu biyu sun shiga fagagen fasaha daban-daban.

 

4246200

 

 

 

captcha