Jaridar Ahal ta habarta cewa, mai kula da masallatai biyu masu alfarma da kuma masallacin manzon Allah (SAW) ya sanar da cewa za a gudanar da wannan karatu ne a lokaci guda tare da shiga watan azumin Ramadan da nufin karfafa alakar al'ummar musulmi da littafin Allah da kuma kafa al'adar tsaka-tsaki a cikin kur'ani mai tsarki.
Wannan shiri dai zai gudana ne daidai da darussan kur'ani na mai kula da Masallacin Harami a shekara ta 1446 bayan hijira domin koyar da kur'ani mai girma da saukakawa haddar da karatun.
Kungiyar kwararrun karatun kur’ani da malaman tajwidi za su kula da darussan kur’ani a masallacin Harami da kuma masallacin Annabi (SAW), da gyaran karatun, da tantance yadda ake amfani da harrufan kur’ani, da koyar da hurumin tajwidi a wadannan darussa.
Wannan shirin zai hada da kafa da'irar haddar kur'ani, da karatun tafsiri, da gyaran karatun kur'ani, da kuma baiwa mahajjata da masu sha'awa damar koyon kur'ani a lokutan ibadar watan Ramadan.
Za a gudanar da tarukan kur'ani na watan Ramadan a babban masallacin juma'a da masallacin Annabi (SAW) a harabar wadannan masallatai, kuma mahajjata da masu aikin umra za su iya amfana da wannan tattaunawa ta hanyar halartar darussa.