Kamar yadda Iqna ta ruwaito; Kafofin yada labaran larabawa sun bayar da labarin yadda ake gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya a duk fadin kasar Iran.
Tashar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, Tehran da wasu wurare 900 na birane da kauyuka na Iran suna gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya.
Rahoton ya bayyana cewa: Tun da sanyin safiyar yau ne aka fara gudanar da tattakin ranar Qudus a duk fadin kasar Iran tare da halartar jama'a da kuma taken "Ya Kudus, mun kasance masu gaskiya da alkawarin da muka dauka." Mahalarta taron sun tashi daga masallatai da manyan filayen garuruwansu da kauyukansu zuwa wurin sallar Juma'a. Mazauna Mashhad da Tehran su ma sun halarci wannan tattaki tun da sanyin safiyar yau.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Masirah na kasar Yemen cewa, al'ummar Iran sun halarci wannan jerin gwano a fadin kasar.
Kungiyar Al-Ahed ta kuma fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna irin goyon bayan da al'ummar Iran suke ba wa al'ummar Palastinu da ake zalunta.