IQNA

Jami'ar Emirati Ta Bude Cibiyoyin Haddar kur'ani A Uganda, Kenya, Comoros

16:30 - April 17, 2025
Lambar Labari: 3493109
IQNA – Jami’ar Al Qasimiya (AQU) ta kaddamar da makarantun haddar kur’ani da dama a gabashin Afirka, tare da bude sabbin cibiyoyi a kasashen Uganda, Kenya, da Comoros.

Shirin ya biyo bayan umarnin da Sheikh Dr. Sultan bin Mohammed Al Qasimi, Sarkin Sharjah kuma dan majalisar koli ya bayar na fadada ilimin kur'ani a fadin nahiyar.

A Moroni, babban birnin Comoros, AQU ta kaddamar da "Makarantar Ilimi ta Rifqa," wadda aka yi wa lakabi da marigayi dalibar jami'a Rifqa Yousef. Bikin ya samu halartar Juma Rashid Al Rumaithi, jakadan UAE a Comoros, tare da jami'an yankin. Makarantar ta ƙunshi ɗakin karatu tare da albarkatun Kalimat Foundation.

An bude irin wadannan cibiyoyi a Nairobi, Kenya, da Kampala, Uganda.

Shirye-shiryen na da nufin tallafawa karatun kur'ani tare da karfafa tattaunawa tsakanin al'adu da wayar da kan jama'a, a cewar kamfanin dillancin labaran Emirates.

 

 

3492691

 

 

captcha