IQNA

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai hari kan dakarun Syria

15:41 - May 30, 2025
Lambar Labari: 3493337
IQNA - Kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS ta dauki alhakin harin farko kan dakarun da ke da alaka da gwamnatin rikon kwaryar kasar Siriya a cikin wata sanarwa da ta fitar.

A cewar Rai al-Youm, kungiyar ta'addanci ta ISIS ta sanar da cewa dakarunta sun dasa bam a kan hanyar sojojin Siriya a lardin Sweida.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasar Syria ta kuma sanar da cewa, a harin farko da kungiyar ta'addanci ta Da'esh ta kai kan sojojin kasar Siriya bayan kifar da gwamnatin Bashar Assad, an kashe wani sojan birged ta 70 na Siriya tare da jikkata wasu uku.

A cewar rahoton, bam din ya tashi ne a kan hanyar motar sintiri kuma wanda ya mutu yana cikin motar.

Ko da yake ba kasafai ake kai hare-haren ISIS a yankunan da sabuwar gwamnatin Syriar da ta karbi mulki bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disambar bara, amma kungiyar na ci gaba da kai hare-hare kan dakarun Kurdawa a arewa maso gabashin Syria.

Dangane da haka ne hukumomin Syria suka sanar a wannan makon cewa sun kame wasu ‘yan kungiyar da ke da alaka da ISIS a kusa da Damascus.

 

 

4285434

 

captcha