A cewar Rossiya El-Youm, a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashe 20 na Larabawa da na Islama sun jaddada wajibcin mutunta ikon kasa da kasa, da ka'idojin kyakkyawar makwabtaka da warware takaddama cikin lumana.
Ta hanyar fitar da sanarwar hadin gwiwa, Ministocin harkokin wajen wadannan kasashen sun bayyana matukar damuwarsu kan wannan lamari mai cike da hadari, wanda ke da babban sakamako ga tsaro da zaman lafiyar yankin baki daya, tare da jaddada bukatar dakatar da ayyukan kiyayya da Isra'ila ke yi kan Iran a daidai lokacin da yankin Gabas ta tsakiya ke fuskantar karin tashe-tashen hankula.
Wadannan kasashe, yayin da suke jaddada muhimmancin kokarin da ake yi na rage zaman dar-dar, domin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da cikakken zaman lafiya, sun jaddada muhimmancin 'yantar da yankin gabas ta tsakiya daga makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi, bisa ga kudurorin kasa da kasa da suka dace, ba tare da nuna bambanci ba, da kuma bukatar dukkan kasashen yankin da su gaggauta shiga cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Sanarwar ta kuma kara jaddada wajabcin kin kai hari kan cibiyoyin nukiliyar da ke karkashin kariya ta hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, bisa ga kudurorin hukumar da kuma kudurorin kwamitin sulhun da suka dace, saboda karara karya dokokin kasa da kasa da dokokin jin kai na kasa da kasa bisa yarjejeniyar Geneva ta shekara ta 1949, tare da yin ishara da bukatar komawa kan hanyar yin shawarwari da wuri-wuri a matsayin hanya daya tilo da za a iya cimma yarjejeniya mai dorewa kan shirin nukiliyar Iran.
Ministocin harkokin wajen wadannan kasashe sun jaddada muhimmancin mutunta 'yancin zirga-zirga a magudanan ruwa na kasa da kasa bisa ka'idojin da suka dace na dokokin kasa da kasa da kuma rashin dakile tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa.
Har ila yau, sun bayyana cewa, mafita daya tilo da za a magance rikice-rikicen yankin, ita ce ta hanyar diflomasiyya, tattaunawa, da kuma kiyaye ka'idojin kyakkyawar makwabtaka bisa ka'idojin dokokin kasa da kasa da na MDD, kuma suna ganin ba za a iya warware rikicin da ake fama da shi ta hanyar soja ba.