IQNA

Wasikar Hizbullah zuwa ga Paparoma: Gwamnatin Sahayoniya na barazana ga zaman lafiyar yankin

22:32 - November 30, 2025
Lambar Labari: 3494272
IQNA - A wata wasika da ta aikewa shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, Hizbullah ta yi Allah wadai da ci gaba da cin zarafi da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da yi a Gaza da Lebanon, yayin da take maraba da ziyarar da ya shirya kai wa Labanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahed cewa, bayan shirin kai ziyara da shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Leo na 14 ya kai kasar, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana maraba da ita a cikin wata wasika da ta aike masa a hukumance, inda ta bayyana kasar Lebanon a matsayin kasa mai bambancin addini da al'adu, wadda a cewar Paparoma John Paul na biyu sako ne ga duniya kuma abin koyi na zaman tare tsakanin addinai da mutane.

Wasikar ta jaddada cewa mutunta mutum da hakkokinsa ba wai kawai ya hada da daidaikun mutane ba, har ma da kasashe, kuma halin ko in kula da wasu kasashe ke yi kan hakkin wasu kasashe ne ya haddasa yake-yake da rikice-rikicen da duniya ke fuskanta a yau.

Kungiyar Hizbullah ta ci gaba da yin ishara da abubuwan da suka faru a Gaza cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ta bayyana hakan a matsayin kisan kiyashi da aka tsara, tare da jaddada cewa irin wahalhalun da al'ummar Palastinu suke fuskanta shi ne sakamakon 'yan mamaya na yahudawan sahyoniya suke tauye hakkinsu na kasarsu da gidajensu da makomarsu da kuma rashin adalcin tsarin kasa da kasa.

Har ila yau kungiyar ta yi ishara da yadda gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da kai hare-hare a kasar Labanon tare da bayyana cewa, manufar wadannan ayyuka ita ce mamaye albarkatun kasa, ruwa, da iskar gas na kasar Labanon da kuma dora bukatun siyasa da tsaro kan al'ummar Lebanon.

Wasikar ta ci gaba da cewa: Gwamnatin yahudawan sahyoniya tare da goyon bayan wasu manyan kasashe suna yin watsi da hakkin al'ummomin yankin tare da yin barazana ga tsaro da zaman lafiyarsu.

A wani bangare na wasikar, kungiyar Hizbullah ta jaddada cewa: Mun kuduri aniyar zaman tare, da wanzar da zaman lafiya a cikin gida, da kuma kare ikon mallakar kasa, kuma za mu fuskanci duk wata mamaya da wuce gona da iri tare da jama'a da jami'an tsaron kasar.

A karshe kungiyar Hizbullah ta yi jawabi ga Paparoma Leo na 14, inda ta sanar da cewa, tana sa ran matsayinsa na goyon bayan adalci, zaman lafiya, 'yanci da kuma kare bil'adama daga zalunci zai kasance a fili da tasiri.

Paparoma Leo na 14, wanda ya yi tattaki zuwa Turkiyya, ana sa ran zai isa Lebanon a gobe Lahadi.

Ganawa da shugabannin siyasa da na addini, duba yanayin zamantakewa da na addini a Labanon, da jaddada bukatar kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya na daga cikin muhimman batutuwan da Paparoma ya mayar da hankali a kai a birnin Beirut.

 

 

 

4319864

 

 

captcha