
A cikin shafinsa na dandalin X Ofishin jakadancin Iran a kasar Ghana ya mayar da martani kan cin zarafin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa shugaban mabiya addinin kirista na darikar Katolika.
Bayanin ya ce abin da Trump ya yi cin zarafi ne mai muni wanda ya ketare dukkanin iyakoki, kuma matakin da Firayi ministar kasar Italiya ta dauka kan batun ya yi daidai.
Trump ya yi kalaman batunci ga Paparoma Leon ne bayan da ya soki hoton da ya saka a shafinsa na yin izgili ga annabi Isa, lamarin da ya fuskanci martani daga paparoma da fadar Vatican.
Bayanin ya kara da cewa, abin da yake faruwa shi ne zai kara fito da komai a fili game da abin da Trump ya yi kan Iran, da kuma yadda yake yin barazanar shafe tarihin Iran wanda ya haura shekaru 7000.
4346631