IQNA

Imam Khomeini ® Ya So Al'umma Ta Yi Wa Kanta Gyara Karkashin Kur'ani

Bangaren kasa da kasa; Imam Khomeini ® ta hanyar wayar da kai da fadakarwa ya so tada al'ummar musulmi daga barci karkashin dogaro da ayar da ke Magana kan cewa hakika Allah bay a canjawa wata al'umma har sai ta canjawa kanta da kanta.
Hujjatul Islama Fu'ad Kazim Almukdadi babban sakataren kungiyar malumman addinin musulunci a Iraki a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ya yi wannan bayani da cewa: Imam Khomeini ® karkashin aya ta 11 a cikin suratul Ra'ad ya yi kokarin tada al'ummar musulmi daga barci da fadakar da su muhimmancin kawo canji a tsakaninsu kafin Allah ya kawo masu irin wannan canji a rayuwarsu da kuma wayewarsu.

416582