IQNA

An Bankado Wani Yunkurin Yin Amfani Da Makamai Masu Guba A Syria

23:45 - August 25, 2018
Lambar Labari: 3482926
Bangaren kasa da kasa, Ma'aikatar tsaron Rasha ta bankado wasu bayanan sirri da suke tabbatar da cewa, ana  shirin sake yin amfani da makamai masu guba a Syria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, wasu kungiyoyin 'yan ta'adda da suke Syria sun shirya tsaf domin yin amfani da makamai masu guba a cikin Syria tare da taimakon Amurka, Birtaniya da kuma Faransa, kuma za a tuhumi gwamnatin Syria ne da yin hakan, domin samun hujjar kai mata hari.

Bayanin ma'aikatar tsaron kasar Rasha ya ce, yanzu haka wani babban jirgin ruwan yaki na Amurka USS Sullivan ya shigo cikin yankin gabas ta tsakiya, kuma ya sauke wani jirgin mai jefa bama-bamai samfurin B-1B a wata kasa da ke yankin tekun fasha.

Rahoton ya ce wadannan kasashe suna son su sake maimaita wasan kwaikwayon da suka shirya ne a 'yan watanni baya tare da kungiyoyin 'yan ta'adda, a lokacin da sojojin Syria suka fitar da su daga yankin Ghota, inda yanzu kuma sojojin Syria suke shirin fitar da 'yan ta'adda daga babbar tungarsu da ke Idlib, kuma a nan ne ake son yin amfani da wadannan makamai a kan jama'a fararen hula, domin a karya gwiwar sojojin kasar Syria.

3741022

 

 

 

 

 

 

captcha