IQNA

Taron Cika shekaru Hudu Da Kama sheikh Zakzaky A Najeriya

20:55 - December 08, 2019
Lambar Labari: 3484301
An yi wani taro kan cikar shekaru hudu domin bitar batun kame sheikh Zakzaky da ya cika shekaru hudu a tsare.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, cibiyar tallafa wa yaran iyayensu suka rasu a waki’ar shahidan Zariya ta shirya wani taron manema labarai a safiyar yau Lahadi 8 ga watan Disamba a birnin Tehran, wanda 'yar Sheikh Ibrahim Al Zakzaky  Suhaila ta halarta.

Yayin taron ta yi tuni da kisan killan da sojoji sukayi wa almajiran Shehun Malamin a ranar 12 ga watan Disamba 2015.

Taron na cika shekaru hudu da harin da sojojin na Najeriya karkashin jagorancin babban hafsan sojin Najeriya Tukur Burutai suka kai a Zariya.

Yayin taron Suhaila ta bayyana cewa matakin da kotu ta dauka na baya bayan nan ya basu matukar tsoro saboda barazana ce ga lafiyar iyayensu.

Haka nan wanann taro yay i kira ga dukaknin bangarorin da ske fada a ji da su saya bai domin ganin an yi adalci a kan wannan batu.

Gwanatin Najeriya dai tana zargin Sheikh Zakzaky ne da tayar da zaune tsaye ta hanyar abin da kira yunkurin kifar da gwamnati domin kafa gwamnatin musuluncia  kasar, wanda a cewar mahukuntan hakan na a matsayin babban laifi na neman durkusar da kasar.

Malamin dai ya sha nanata cewa shi kiransa na zaman lafiya ne, kuma baya tayar da hankalin kowa domin kuwa bait aba daukar makamai domin yaki da gwamnati ko wani ba.

 

 

 

 

 

3862489

 

 

captcha