IQNA

Yanayin Watan Ramadan A Arewacin Amurka

23:57 - April 13, 2021
Lambar Labari: 3485805
Tehran (IQNA) kamar kowace sheakara a yankunan arewacin Amurka a lokacin watan ramadan musulmi suna gudanar da wasu harkokinsu na zumi da ibada.

Shafin abbott Islam ya bayar da rahoton cewa, a yankunan arewacin Amurka a lokacin watan ramadan musulmi suna gudanar da wasu harkokinsu na zumi da ibada kamar kowace sheakara.

A yau Firayi ministan kasar Canada Justin Trudeau ya gabatar da bayani wanda aka saka a kafofin yada labarai na gwamnatin kasar Canada, inda yake taya dukkanin musulmi na kasar da ma na duniya baki daya murnar shiga watan ramadan mai alfarma.

A wannan kasar musulmi da kiristoci suna da girmama juna tare da taya juna murna a duk lokacin da wani daga cikinsu yake murnar wani ab una bikin shekara ko kuma wani lamari da ya shafi addini.

A lokacin buda baki, musulmi sukan gayyaci makwabtansu kiristoci domin su zo su ci abinci tare da su, inda a kan gayyaci wadanda ba musulmi har a masallatai domin yin buda baki tare da musulmi.

Irin wannan matsaya da salo da musulmin kasar Canada suke dauka, ya taimaka matuka wajen rage kaifin yunkurin masu tsananin adawa da addinin muslunci, inda duk lokacin da suka bukaci goyon bayan jama’a domin cutar da musulmi, jama’a ba su basu goyon baya.

A wasu manyan shaguna na biranan kasar ta Canada, ana sayar da kayayyakin da musulmi suke yin amfani da su a lokacin azumin watan ramadan, wanda hakan ke nuni da irin yadda ake bayar da muhimmanci ga lamarin musulmi da kuma lokutan ibadarsu a wannan kasa.

 

3964194

 

captcha