IQNA

Bayyana Sirrin Wani Tamkar Kisan Kai na Ganganci Ne

Tehran (IQNA) Imam Sadeq (AS) yaa cewa; duk wanda ya bayyana sirrinmu tamkar ya kashe mu ne ba kuma kisa na kure ba kisa na ganganci.

A jawaban da yake gabatarwa tun daga farkon watan Muharram dangane da juyayin Ashura Dr Mohsen Esmaeili ya yi karin bayani a kan wani batu da cewa; wannan yana koyar da mu ne muhimmancin rike sirrin jama'a, domin kuwa bayyana sirrin mutane zai iya sa rayuwarsu cikin hadarin da za su iya rasa rayuwarsu saboda hakan.

 

3475564