Masallacin Dimaukum: Alamar Salon Gini A Philippines
TEHRAN (IQNA) - Masallacin Dimaukum yana cikin wuraren bude ido na Philippines, wanda yake cikin gundumar Maguindanao.
An kaddamar da masallacin a shekara ta 2014, an yi masa mai launin ruwan hoda domin alamta zaman lafiya kuma ma'aikata ne suka gina shi domin nuna alamar hadin kai da 'yan uwantaka tsakanin addinai.