
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakato daga tashar talabijin ta Almanar cewa, daya daga cikin yan majlaisar dokokin kasar Lebanon karkashin kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah Hassan fadlollah ya bayyana cewa, dole ne a kafa wata kungiya mai karfi wadda ta zata hada dukkanin bangarorin musulmi a kasar Lebanon domin yaki da mummunar akidar da ta bulla ta kafirta musulmi ba gaira ba sabar.
Dan majalisar ya ci gaba da cewa bisa lala'akari da cewa bullar iri wadannan kungiyoyi yana da babban hadari ga al'ummar musulmi baki daya da ma saran mabiya addinai dab a na musulunci ba, ya zama wajibi musulmi su safke nauyin day a rataya akansu wajen fuskantar wadannan dabbobin da ke rayuwa cikin mutane suna karba sunan musulmi.
Ya kara da cewa idan aka yi la'akari da ayyukan ta'addancin da wadannan mutane suke aikatawa, za a ga cewa musulmi ne suka fi cutuwa fiye da kowa, yayin da sauran mabiya addinai ma bas u tsira ba, kuma wannan yana bata sunan addinin muslunci a idon duniya.